Shugaban na Amurka ya yanke wannan shawara ne saboda ci gaba da kai hare hare da kungiyar ‘yan ta’addan ta ke yi a cikin kasar Afghanistan.
“Mu na so mu ga sun iya cika alkawuransu” na kawo karshen tashe-tashen hankula a kasar da yaki ya daidaita kafin a “Saka musu” da ganawa da Trump," abin da Pompeo ya fada kenan a gidan talabijin na CNN. Sai dai bai bayar da tabbacin ko za a dawo da tattaunawar ko lokacin da za a yi ba.
Babban jami’in diflomasiyyar Amurka din ya ce Trump ya shirya ganawar jiya Lahadi a makebarsa ta Camp David da ke wajen birnin Washington da kungiyar Taliban da kuma Shugaban Afghanistan, Ashraf Ghani, ko da yake dama daban daban za a yi ganawar, wadda aka shirya bisa imanin cewa hakan zai "kare muradun Amurka” don kawo karshen ayyukan da Amurka ta shafe shekaru sha takwas ta na yi a Afghanistan.