Kasuwar Amurka ta dan mike a jiya Alhamis biyo labarin amincewar da Amurka da China suka yi na gudanar da tattaunawar cinikayya.
Kasuwar hannu jari ta Dow Jones ta samu bunkasa da maki 372. Kasuwar S&P 500 itama ta tashi da kashi daya cikin darin, yayin da kasuwar NASDAQ ita kuma ta tashi da kashi biyu cikin dari
Sabbin haraji akan kayayyakin Amurka da China da kuma rashin tabbas da yake damun ‘yan kasuwa a cikin wannan lokaci ka iya zuwa karshe idan aka gudanar da gagarumar tattaunawa.
Da safiyar jiya Alhamis ne China ta sanar cewa Washington zata shirya wani babbar tattaunawa a farkon watan Oktoba.
Ma’aikatar kasuwanci ta Beijing, ta fada cewa mataimakin Firaimiya, Liu He, da wakilin Amurka akan cinikayya, Robert Lightizer, da kuma sakataren baitalmalin Amurka, Steven Mnuchin, sun amince da shirya ganawa a wata hirar tarho da su ka yi.
Ofishin wakilan kasuwancin bai bada takamaiman ranar taron ba, sai dai kawai ya ce akwai taro a ‘yan makwanaki masu zuwa.
Bangarorin biyu za su gudanar da kwarya-kwaryar tattaunawa a cikin wannan wata, wanda China ta ce zata gabatar da wani tsari da zai kai ga samun nasara.
Sai dai babu wata muhimmiyar tattaunawa tsakanin Amurka da China tun cikin watan Yuli.
Facebook Forum