Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya soke wata ganawar sirri da suka shirya yi yau Lahadi da shugaban Afghanistan Ashraf Ghani da wasu manyan shugabannin kungiyar Taliban a Camp David, wato wani kebabben wuri don shugaban Amurka.
A wasu jerin sakonni da ya rubuta a shafinsa na Twitter jiya Asabar da yamma, Trump ya bayyana cewa ya soke shirin ganawar a Camp David dake jihar Maryland ba tare da bata lokaci ba biyo bayan wani harin bom na mota da aka kai a birnin Kabul wanda yayi sanadiyar kisan mutane 12, ciki har da wani sojan Amurka.
Shugaban ya kara da cewa idan har ‘yan Taliban ba za su iya amincewa su tsagaita wuta ba a wannan muhimmin lokacin da ake ganawar neman sulhu, har ma suka kashe bayin Allah guda 12, to ta yiwu ma ba su da karfin ikon da za a yi wasu shawarwarin cimma wata yarjejeniya mai ma’ana da su. Har nan da shekaru nawa suke so su yi ta yaki? A cewar Trump.
Wadannan sakonnin na twitter da Trump ya rubuta tabbas ba a yi zaton su ba a game da batun shawarwarin da aka ci gaba da yi a birnin Doha na kasar Qatar tsakanin jami’an Amurka da ‘yan Taliban, tattaunawar da kungiyar mayakan ta bayyana a matsayin mai muhimmanci, a cewar David Sedney, mukaddashin shugaban jami’ar Amurka dake Afghanistan.
Facebook Forum