Wannan zargi na zuwa ne yayin da hukumomin kasar ta Amurka ke gudanar da bincike kan satar bayanan da ya shafi hukumomin tarayyar kasar.
Sakataren Baitul malin Amurka, Jack Lew, ya bayyana hakan ne a jiya Talata yayin da kasashen biyu ke gudanar da wani muhimmin taro a tsakaninsu kan batutuwan da suka shafi tsaro da tattalin arziki.
Mr Lew, ya nanata damuwarsa kan abin da ya ce gwamnatin China ce ta dauki nauyin gudanar da satar bayanan.
A jawabin nasa, Mr Lew bai fito karara ya bayyana irin girman satar bayanan ba, wanda aka gano a farkon watan nan, inda aka saci muhimman bayanan ma’aikatan Amurka da ke aiki yanzu da kuma wadanda suka bar aiki.
Gwamnatin shugaba Barack Obama dai ba ta fito fili ta dora alhakin satan akan China ba, sai dai jami’an kasar da dama, sun ba da tabbacin cewa Chinan ce ke da alhaki.
Gabanin fara zaman tsakanin Amurkan da China a nan Washington, wani babban jami’in Amurka ya bayyana cewa za su fito karara su tunkari Chinan game da wannan batu na satar bayanan.