Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AMURKA: An Tura Wani Dan Sanda Farar Fata Hutun Dole a Jihar Texas


Zanga-zanga domin a kawo karshen muzgunawar da 'yansanda suke yiwa jama'a musamman bakake
Zanga-zanga domin a kawo karshen muzgunawar da 'yansanda suke yiwa jama'a musamman bakake

Wani dan sanda farar fata da yayi kokarin harbe yara matasa ya tafi hutun dole a jihar Texas

Mahukunta anan Amurka sun tura wani dan sanda farar fata zuwa hutun dole bayan an ganshi sailin da yake kokarin fito da bindiga domin ya fatattaki wasu yara matasa wadanda bakake ne.

Wannan lamarin dai ya faru ne a kudancin Amurka a cikin jihar Texas, anga dan sandan yana kokuwa da daya daga ciin wadannan yaran kuma ya kada ta, wanda wannan shine tursasawa na baya-bayan nan da ake tuhumar aikata shi sakamakon banbancin launin fata.

Wannan abu da ya faru ranar asabar 6 ga wannan watan a birnin Mckinney, dake kilomita 50 daga arewacin Dallas.

Rundunar yan sanda sun dauki matakin ne biyo bayan koken da al’umma suka kai.

Shi dai wannan dan sanda mai suna Eric Casebolt an ganshi yana gudu yana bin wadannan yaran matasa kafin daga bisani ya samu ya cafke guda daga cikin su bayan ya kada ta kasa nan take kuma ya buga mata ankwa.

Yarinyar yar shekaru 15 mai suna Dajarria Becton, ta shaidawa wani gidan talkabijin cewa dan sandan ya kama ya murde mata hannu kana yayi mata gashi kamar linzamin doki

XS
SM
MD
LG