Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Nazarin Yiwuwar Girke Manyan Makaman Yakinta A Baltic Da Turai


Wani jirgin ruwan dakon jiragen yaki na Amurka
Wani jirgin ruwan dakon jiragen yaki na Amurka

Yayin da dangantaka tsakanin Amurka da Rasha ke kara tsami, Amurka na duba yiwuwar jibge wasu manyan makaman yakinta a Turai da Baltic don tauna tsakuwa

Amurka na duba yiwuwar girke manyan makaman soji a kasashe da dama na yankin Baltic da Turai, a cewar wasu jami'an gwamnati jiya Asabar.

An ce wannan shawarar ta nuna ma Shugaban Rasha Vladimir Putin cewa Amurka za ta kare kawayanta na kawancen NATO a gabashin Turai.

Jaridar New York Times ce ta fara bayyana wannan al'amarin a jiya Asabar.

Muddun aka amince da wannan shawarar, za a girke wasu daga cikin makaman ne a wasu kasashe da dama da ada ke karkashin tsaohuwar Tarayyar Soviet, a karo na farko tun bayan yakin cacar baka.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG