Amurka, da Mexico, da Canada zasu sake hawa teburin tattaunawa yau Laraba don yiwa yarjejeniyar cinikayyar babu tsangwama dake tsakaninsu garambawul, yarjejeniyar da aka cimma a shekarar 1994, wacce ta zama babbar abun suka a lokacin yakin neman zaben shugaba Donald Trump.
Trump ya bayyana wannan yarjejeniyar da ake kira NAFTA a takaice a matsayin yarjejeniya mafi muni a tarihin duniya, wadda bata yiwa Amurka adalciba, yayinda ta bar ayyukan masana’antu dayawa suka koma Mexico.
Duba yadda za a cike gibin muhimmin abu ne ga Amurka a tattaunawar da za a yi, tare da neman yadda za a kawas da hanya ko tsarin sasantawa da kasashen uku ke amfani da ita wajen sasanta duk wata takaddama da ta taso tsakaninsu.
Wakilai da zasu yi ganawar zasu yi zama dabam-dabam don neman canje-canjen da zasu taimaka masu kammala aikinsu kafin karshen shekarar nan. Idan har zaman ya kai ga shekarar 2018, akwai fargabar shawarwarin zasu fuskanci sarkakiya saboda zaben shugaban kasar Mexico da na ‘yan majalissar tarayyar Amurka dake tafe a shekarar ta 2018.