Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatar Shari'ar Amurka Na Binciken Mummunar Zanga-zangar Fifita Jinsin Turawa


Biyo bayan baiwa hammata iska da aka yi a taron gangamin turawa jar fata masu fifita jinsin turawa da kuma ‘yan zanga zangar da suka fito yin adawa da wannan gangamin a Jihar Virginia, an fara gudanar da bincike kan wani mai mota da ya kashe wata mata.

Ma’aikatar shari’a ta tarayya a nan Amurka ta fara binciken keta hakkin bil Adama dangane da wata motar da aka tuka cikin mutane har ta kashe mutum guda a wajen wata zanga zangar nuna kin jinin gangamin da Turawa ‘yan wariyar launin fata suka shirya a garin Charlottesville dake Jihar Virginia.

Atoni-janar na tarayya, Jeff Sessions, yace wannan tashin hankali da mace-mace a Charlottesville, farmaki ne na kai tsaye kan tsarin doka da shari’a na Amurka. Sessions yace idan irin wannan abu ya samo asali daga akidar gaba ko kin jinin wani jinsi, to ya zamo abinda ya saba da akida da dabi’un Amurka, kuma ba a lamunta da shi ba.

Gwamna Terry McAuliffe na Jihar Virginia ya ayyana kafa dokar ta baci a bayan da aka fara ba hammata iska a tsakanin turawa ‘yan wariyar launin fata da suka sanya sulke kuma suna dauke da garkuwa wadanda suka je gangamin nuna rashin yarda da kokarin cire mutum mutumin wani shugaban ‘yan awaren Amurka, da kuma wasu mutanen da su ma suka yi irin wannan shiga suka je wurin domin gangamin nuna kin jinin masu wariyar launin fatar a garin Charlottesville.

Gwamna McAuliffe yayi tur da masu wariyar launin fatar da suka taru daga jihohi dabam dabam, inda yace, “Sako na ga turawa ‘yan fifita jinsin jar fata da ‘yan ra’ayin wariyar launin fata ‘yan akidar Nazi da suka taru yau a Charlottesville, shine, ku koma inda kuka fito, ba mu bukatarku a jiharmu. Ku marasa kunya ne.”

Daga bisani, gwamnan ya rubuta sako a shafinsa na Twitter inda yake cewa, “Abubuwa da kuma kalamun da aka ji aka gani cikin sa’o’I 24 da suka shige a Charlottesville, ba karbabbu ba ne, tilas kuma a daina su. ‘Yancin fadin albarkacin baki, ba wai ‘yanci ne na tayar da fitina ba.”

Shi ma shugaba Donald Trump yayi Allah wadarai da abinda ya kira “nuna gaba, kin jinin wasu jinsi da kuma tashin hankalin da aka gani a Charlottesville daga bangarori dabam dabam.

Sai dai kuma TYrump ya sha caccaka daga wurin ‘yan jam’iyyarsa ta Republican da kuma ‘yan Democrat a saboda ya ki fitowa cikin wannan jawabi nasa yayi tur da Turawa ‘yan wariyar launin fata.

Sanata Orin Hatch dan Republican daga Jihar Utah, yace, “tilas ne a kira Shaidan da sunansa na Shaidan. Dan’uwana ya rasa ransa wajen yakar Hitila saboda akidarsa ta ‘yan Nazi, amma kuma ga irin wannan akida a cikin gida wadda tilas mu kalubalance ta.

Jim kadan a bayan da jhukumomin Jihar Virginia suka soke wannan gangami na turawa ‘yan wariyar launin fata jiya, sai aka ga wata mota da gudu ta doshi taron mutanen da suka je nuna kin jinin wannan gangami na ‘yan wariyar launin fatar. An ga yadda motar ta doke mutane suna yin sama suna fadowa kasa.

An kashe wata mata mai shekaru 32 da haihuwa, wasu kimanin dozin biyu suka ji rauni.

‘Yan sandan garin Charlottesville suka ce sun damke direban wannan mota mai suna James Alex Fields Jr, dan shekaru 20 da haihuwa, daga Jihar Ohio.

Sa’o’i a bayan nan, rundunar ‘yan sandan Jihar Virginia ta ce wani jirgin samanta na helkwafta dake aikin sanya idanu kan wannan gangamin, ya fado a cikin wasu bishiyoyi a bayan gari ya kashe ‘yan sanda biyu dake cikinsa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG