Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliya Ta Halaka Fiyeda Mutane 30 A Nepal.


wasu 'yan kasar Nepal a wani kauye suke kallon ruwa na gudu.
wasu 'yan kasar Nepal a wani kauye suke kallon ruwa na gudu.

Tuni aka umarci sojoji da 'Yansanda da farar hula su fara aikin ceto wadnda suka makale kan gine gine

Rahotanni daga Nepal sun ce ambaliyar ruwa da gocewar laka sun halaka fiyeda mutane 30 sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwariya da aka yi a yankin cikin sa'o'i 24 da suka wuce, kamar yadda hukumomin kasar suka fada jiya Asabar.

Jami'an kasar suka ce mutane 10 sun bata, kuma akwai alamun yawan wadanda suka hakala zai karu, ganin ruwa ya mamaye kasar baki daya.

An tura tawagar masu aikin ceto daga cikin sojoji da 'yansanda da farar hula domin ceto wadanda suka makale akan rufin gine-gine, ko akan tuddai, inji jami'an gwamnati, yayinda hotunan talabijin suka nuna hotunan hanyoyi da gadoji da ambaliyar ta lalata.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG