Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Colombia Ta Kalubalanci Trump Kan Barazanar Daukan Matakin Soji a Venezuela


Shugaban Colombia Juan Manuel Santos, (hagu) yana magana da manema labarai yayin da mataimakin shugaban Amurka Mike Pence (dama) yake sauraro a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da suka yi a ranar 13 ga watan Agusta, 2017.
Shugaban Colombia Juan Manuel Santos, (hagu) yana magana da manema labarai yayin da mataimakin shugaban Amurka Mike Pence (dama) yake sauraro a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da suka yi a ranar 13 ga watan Agusta, 2017.

Wasu daga cikin shugabannin kasashen yankin Latin Amurka, sun fara maida martani kan barazanar matakin soji da shugaban Amurka Donald trump ya ce zai dauka a kasar Venezuela domin dawo da tsarin mulkin dimokaradiyya.

Shugaban Colombia Juan Manuel Santos ya ce baba wata kasar yankin Latin Amurka da za ta amince da duk wani matakin soji da Amurka ke so ta dauka a Venezuela, kuma a cewarsa, bai ma kamata a fara wani tunanin yin hakan ba.

Santos ya kira taron manema labarai na hadin gwiwa da mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence da ke aikin ziyara.

Shugaban Amurka Donald Trump ya fadi a ranar Jumma'a cewa ba zai kau da yiwuwar amfani da matakin soji don a taimaka a maida tsarin dimokaradiyya a Venezuela ba.

Da ya juya kan matakin soji da Amurka ta taba dauka a fadin Latin Amurka sama da karni guda da ya gabata, sai Santo ya ce babu wani shugaban kasar Latin Amurka da ke sha'awar irin wancen "shirmen" ya sake faruwa.

Ya ce dole ne a bi hanyar lalama wajen maido da dimokaradiyya a Venezuela, ya na mai bayyana nahiyar Amurka da "nahiyar zaman lafiya," wanda ya kamata mu tabbatar da dorewar hakan.

Tun da farko a jiya Lahadin, Shugaban hukumar leken asirin tsaron kasa ta Amurka Mike Pompeo ya fadawa gidan talabijin na FoxNews cewa Trump ya ambaci yiwuwar daukan matakin soji ne don, a cewarsa, "a karfafa ma mutanen Venezuela gwiwa sannan a kuma basu damar samar da yanayin da zai sa dimokaradiyya ta dore."

Kasar Venezuela ta bayyana barazanar Trump a matsayin wuce makadi da rawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG