Hukumomi a kasar Nepal sun ce ambaliyar ruwa da gocewar laka daga kan tuddai da suka wakana a sanadin ruwan sama kamar da bakin kwarya sun kashe mutane fiye da 30 a kasar.
Wasu mutanen 10 sun bace yayin da adadin wadanda suka mutu zai iya karuwa saboda ruwa ya malale sassa da yawa na kasar.
Masana yanayi sun yi has ashen cewa za a samu Karin ruwan sama cikin dare, yayin da gwamnati ta gaergadi jama’a da su yi hattara. Kogin Koshi dake kudancin kasar ya cika ya tumbatsa, har matsayinsa ya kai yadda hukuma ta shata a zamanin mai hadari.
Ruwan damina da ake samu a kasar daga watan Yuni zuwa Satumba na da matukar muhimmanci ga Nepal wadda ta dogara kan amfanin gona, amma a kowace shekara yana haddasa bala’i.
An tura kungiyoyin ceto da suka kunshi sojoji, ‘yan sanda da farar hula na yanki domin taimakawa mutanen da suka haye kan rufin gidajensu ko suka samu wani tudu suka hau.
Facebook Forum