WASHINGTON, D. C. - Hakan dai ya ninka adadin mace-macen da aka samu makonni biyu da suka gabata yayin da ake samun karuwar ruwan sama musamman a yankin gabar teku da babban birnin kasar Dar es Salaam.
Firaiminista Kassim Majaliwa ya shaidawa majalisar dokokin kasar cewa Sauyin yanayi na El Niño ya kara tabarbarewar damina da ake ci gaba da yi, lamarin da ya haddasa ambaliya tare da lalata tituna, gadoji da jiragen kasa.
An rufe makarantun da ambaliyar ruwa ta yi kamari sannan kuma jami’an agajin gaggawa sun ceto mutanen da ruwan ya rutsa da su.
Majaliwa ya gargadi wadanda ke zaune a yankunan da ke kasa-kasa da su tashi zuwa tuddai, sannan ya bukaci jami’an gundumomi da su tabbatar da cewa abubuwan da aka tanada na agaji a baiwa mabukata cikin wadanda gidajensu ruwa ya tafi da su. Ya ce sama da gidaje 51,000 ne ruwan sama ya shafa.
Yankin gabashin Afirka na fama da ruwan sama kamar da bakin kwarya, inda aka kuma samu ambaliya a makwabtan kasashen Burundi da Kenya.
A kasar Kenya, an bayar da rahoton mutuwar mutum 35 ya zuwa ranar Litinin, kuma ana sa ran adadin zai karu yayin da ake ci gaba da samun ambaliyar ruwa a fadin kasar.
-AP