Ambaliyar Ruwa Na Barazana Ga Jihar Texas

Wani yanki da ambaliyar ruwa ta mamaye a jihar Texas ta Amurka

Bayan da mahaukaciyar guguwar Harvey da ta sauka a yankin Jihar Texas a nan Amurka, yanzu mazauna wasu yankunan jihar na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa yayin da hasashe ya nuna cewa mai yiwu wa a tafka ruwan sama a yankunan.

Ambaliyar ruwa da guguwa mai karfin gaske, na daga cikin matsalolin da yanzu ke fuskantar mazauna kudu maso gabashin jihar Texas da ke nan Amurka, yankin da mahaukaciyar guguwar Harvey mai dauke da ruwan sama ta yi wa dirar mikiya a ranar Juma’a.

Wani hasashen yanayi da aka yi a yankin Houston, ya nuna cewa mai yiwuwa ruwan sama ya sauka a wasu yankuna, a yau Lahadi, wanda ka iya haifar da ambaliyar ruwa.

A halin kuma da ake ciki, hukumar da ke hasashen yanayi ta kasa ta tabbatar da cewa an samu aukuwar guguwa mai karfin gaske har sau bakwai, wadanda suka sauka tun daga ranar Juma’a.

Hukumomin tashar jiragen ruwan da ke jihar ta Texas sun sanar da cewa nan da sa’oi 24 zuwa 48, za su bude gabar tekun yankin, bayan sun kammala auna irin asarar da aka tafka.

A dai ranar juma’a aka rufe tashar, inda aka hana ficewa da shigar jiragen ruwa a bakin dayan yankin.

Ya kuma zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutum guda ne a baki dayan jihar ta Texas sanadiyar wannan bala’i.