Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya gwammace ya zama sanadin samun gagarumar matsalar kasafin kudi maimakon ya kasa iya cika alkawarin da yayi a lokacin yakin neman zabensa, na yin abinda ya kira “Mai Matukar Muhimmanci” wato gina Katanga akan iyakar Amurka da makwabciyarta kasar Mexico.
A lokacin wani gangami mai kama da yakin neman zabe jiya Talata da marraice a birnin Phoenix na jihar Arzona, shugaba Trump ya ce “idan ta kama a rufe ma’aikatun gwamnati, sai mu rufe, amma sai mun gina wannan katangar.” Ya kuma kara da cewa, zabenshi da aka yi a watan Nuwamban bara, Amurkawa sun yi hakan ne don ya dauki matakai akan baki dake shigowa ko wadanda suka shigo kasar.
Sai dai kuma kafin wannan katangar ta ginu, dole ne majalissar dokokin Amurka ta amince da kudaden da za a yi amfani da su wajen gina ta, kuma gashi har ya zuwa yanzu majalissar bata kammala tsara kasafin kudade na shekarar 2018 ba, wadda zata fara aiki daga ranar 1 ga watan Oktoban wannan shekarar. ‘Yan majalissa daga jam’iyyar Democrat na adawa da wannan shirin na gina katagar, abinda ya sa Trump kira su “‘yan hana ruwa gudu” a daren jiya Talata.
Haka kuma shugaban ya yi amfani da wannan damar a gangamin ya caccaki kafafen yada labarai, inda ya kwatanta ‘yan jarida da masu cin amana, ya kira su “mugayen mutanen wadanda basa son kasarmu.”
Facebook Forum