Shugaban Amurka Donald Trump ya yabi, tsohon mai tsara dabaru na Fadar White House, Steve Bannon a shafinsa na Twitter, inda ya ce aiki da mutum kamar Bannon abin alfahri ne.
“Ina so na mika godiya ta ga Steve Bannon saboda irin rawar da ya taka, ya shiga gangamin yakin neman zabe na, a lokacin ina tunkarar Hillary Clinton mara gaskiya, abin alfahari ne, na gode.” Kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Twitter.
Shi ma mataimakin shugaban kasar, Mike Pence, ya yabi Bannon a shafinsa na Twitter a jiya Asabar, inda ya ce yana mika godiyarsa bisa abinda ya kwatanta a matsayin “yadda ya shi Bannon ya yi aiki tsakani da Allah.”
“Steve ya mashugaban Amurka Trump aiki da kwarewa, ina jinjina abotarsa da kuma rawar da ya taka. Na gode Steve." In ji Mike Pence.
Da tsakar ranar Juma’a, Fadar White House ta bayyana cewa Steve zai bar aiki da gwamnatin ta Trump, da kuma yamma har ya koma kafar yada labaran nan ta yanar gizo da ya shugabanta a da, mai suna Breibart wacce ke yada manufofin masu ra’ayin mazan jiya.
Rahotannin sun nuna cewa daga Fadar ta White House Bannon ya wuce kai-tsaye zuwa ofishin na Breibart.
Facebook Forum