Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Guguwar Harvey Ta Sauka a Jihar Texas


Hoton guguwar Harvey da tauraron dan adam ya dakko
Hoton guguwar Harvey da tauraron dan adam ya dakko

Mahaukaciyar guguwar Harvey da ta sauka a yankin Jihar Texas a Amurka ta fara shafar tattalin arzikin kasar, inda farashin man fetur da na iskar gas suka haura.

Shugaban Amurka Donald Trump, ya rattaba hanu tare da ayyana guguwar Harvey nan da ta dumfari jihar Texas a matsayin bala’i, yayin da idon guguwar ya fara kutsa kai a gabar tekun jihar a daren jiya Juma’a, inda karfin guguwar ya shiga rukuni ko kuma aji na hudu.

Hukumar da ke sa ido kan aukuar bala’in guguwa a Amurka, ta bayyana cewa, guguwar na tafiyar kilomita 250 cikin sa’a guda, sannan tana daga igiyar ruwa da tsayinta ya kai taku 13, tare da ayyana lamarin a matsayin “mai barazana ga rayuwa.”

Gwamnan jihar ta Texas, Greg Abbot, ya ce guguwar za ta kasance wata mummunar bala’i, inda ya kuma gargadi al’umar yankin da su zauna cikin shirin fuskantar ambaliyar ruwa, wandda mai yiwu ba a taba ganin irinta ba.

Ita dai wannan guguwar za ta gangaro ne daga yankin birnin Corpus Christi, da ke jihar ta Texas, inda aka yi hasashen za ta yi tafiya da fadin kilomita 600 tare da ratsawa ta gabar tekun Texas cikin dare.

Tun gabanin saukar mahaukaciyar guguwar, tattalin arzikin Amurka ya fara shafuwa, inda farashin man fetur da na iskar gas suka tashi, sannan guguwar ta jefa fargaba a zukatan mutane da dama kan adadin gidajen da guguwar za ta iya shafa, wadanda aka yi kiyasin kudinsu ya kai dala biliyan 40.

Shi dai yankin na Gabar Tekun Mexico na dauke ne da kusan kashi daya cikin biyar na arzikin man fetur din Amurka, sannan kusan rabin matatun man kasar a nan suke.

Sanadiyar wannan guguwa, za a iya samun cikas wajen aikin fitar da mai, da aikin jigilar sauran dangoginsa tare da samun barna akan kayayyakin tace man.

Tuni dai kamfoni masu hakar mai suka kwashe ma’aikanatansu da ke aikin tono mai a kan teku.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG