Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojin Ruwan Amurka 10 Sun Bace Bayan Da jirgin Ruwansu Yayi Karo Da Wani Jirgin 'Yan Kasuwa


Jirgin Ruwan Sojan Amurka na USS John S. McCaine
Jirgin Ruwan Sojan Amurka na USS John S. McCaine

Wasu sojin ruwan Amurka guda goma sun bace wasu biyar kuma suka jikkata bayan da jirgin ruwan sojin Amurka mai suna "USS John S. McCaine" yayi karo da wani jirgin jigilar kayan 'yan kasuwa a gabashin Singapore kusa da tekun Malacca.

Rundunar sojin ruwan Amurka ta fada a wata sanarwa cewar, jirgin na Amurka yayi ci karo ne da daya jirgin mai dauke da tutar kasar Liberia mai suna Alnic MC a daidai karfe 6:20 na safe. Jirgin Amurka na McCaine yana kan hanyarsa ne zuwa Singapore a kan balaguron da ya saba lokacin da hadarin ya faru.


Jirgin na Amruka ya samu nakkasa mai yawa amma dai yayi kokarin isa sansanin sojin ruwan Amurka na Changi a gabar tekun Singapore bayan wasu sa’o’i. Shima daya jibgegen jirgin daukar kayan ya sami lahani amma dai ba dayan ma'aikatansa da ya sami ko kwalzane na rauni.

Wani jirgi mai saukar ungulu na Singapore ya dauke sojojin Amurkan su hudu zuwa wata asibitin kasar don yi musu jinya na raunkuka da suka samu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG