A yayin da jiga-jigen jam’iyyar PDP ke hana idanuwansu rimtsawa, a yunkurinsu na dinke barakar da ta tarwatsa jam’iyyar gida biyu, a gefe daya matasa masu goyon bayan sabuwa da kuma tsohuwar PDP suna bayanna ra’ayoyinsu akan wannan baraka da aka samu a jam’iyyar.
Alhaji Yelwa Abubakar wanda aka fi sani da suna Dawa Cali, yana bangaren sabuwar PDP ne. Yace “PDP ta riga ta makara, to tun-tuni muna gaya musu, saboda haka rigima ne akeyi da wanda tun tashinsha, akwai salo da zare a hannunsa shine Atiku (Abubakar). To amma ka sani, mu kananan ‘yan jam’iyyar PDP mun wuce sanin hadisi. Tunda basu yi mana sanyi ba, suma ai sanyin ba zai same su ba. Su suka san inda suka dauko, kuma su suka san inda zasu dire. Mu ko namu ai, an dora mana kaya ne da gammo, kuma idan an sauke muna shirin hutawa."
Shi kuwa mai goyon bayan sabuwar PDP Rabi’u Muhammad, yace wasu mutane ne suke amfani da wannan yanayi. “Wasu ne kawai suke so suyi amfani da wannan dama, su cimma burin bukatun kansu. Mu matasa, kanmu ya riga ya waye. Babu wani wanda zai yi amfani da wnai buguzum yazo ya cimma wani burinsa wanda ba don jama’a yakeyi ba. Kuma shi Bamangan nan, mun tabbatar da cewa duk abinda zai kawo masalaha a jam’iyyar nan zai yi. Amma maganar a ce ya sauka kafin ayi sulhu, wannan ba magana bane.

Your browser doesn’t support HTML5