Gwamnatin bata bada wata hujja ba akan dalilin da yasa Shugaban, dan jam’iyyar PDP ya sallami wadannan mutane ba, amma masu hasashe na gani an yi haka ne saboda ministocin suna da alaqa kai tsaye, ko ta gefe da gwamnonin nan su 8 da suka bijire wa gwamnati.
Akwai wasu ministoci ma da aka ce an samu korafe-korafe daga jihohinsu dake cewa basa kula da aiki. Wannan ma na daga cikin dalilan da ake tunanin sun saka Shugaba Goodluck ya sallami wadannan ministoci.
A halin yanzu dai, jam’iyyar Shugaba Goodluck Jonathan ta PDP na fama da matsalolin cikin gida, inda wasu gwamnoni da ‘ya’yan jam’iyyar suka balle suka bar shugabancin jam’iyyar karkashin Bamanga Tukur, suka koma wani sabon PDP karkashin shugabancin Kawu Baraje.