WASHINGTON, DC —
Gwamnoni bakwai da suka balle daga jam'iyyar PDP suka kafa wata sabuwa katkashin inuwar shugabancin Kawu Baraje sun mayarda martani dangane da rufe hekwatarsu da jami'an tsaro suka yi kamar yadda Bamanga Tukur ya ce zasu yi.
A martanin da suka mayar gwamna Murtala Nyako na jihar Adamawa ya ce duk da barazanar da aka yi masu a shirye suke su kare martabar Najeriya. Gwamnonin sun ce babu mamaki irin matakan da Bamanga Tukur da shugaba Goodluck suka dauka to amma sun shirya su kalubali duk wata barazana. A wata sabuwa kuma tuni bamgaren Bamanga Tukur ya yabawa jami'an tsaro da matakan da suka dauka. Haka kuma an janye dogarawan gwamna Amechi na jihar Rivers.
Alhaji Hallu Hama Jodi ya ce duk takardamar ta kare ne kan abun da za'a ci, wato akwai kwadayi cikin lamarin. Su kuma talakawa suna kokawa suna cewa rikicin da aka soma a jiharsu da yanzu ya zama na kasa gaba daya yana komawa kansu domin rashin cigaba a jihar.
Ga karin bayani