A jihohin Bauchi da Gombe shirin kafa ofisoshin sabuwar PDP ya yi nisa. Alhaji Mohammed Lawal Isa shi ne shugaban jihar Bauchi. Ya shaidawa Murya Amurka cewa sun zagaya duk kananan hukumomin jihar ashirin da biyu domin su nemi ra'ayoyin mutane. Ya ce mutane sun fito kwansu da kwakwatarsu suna goyon bayan jam'iyyar a karashin jagorancin Alhaji Kawu Baraje. Ya ce suna tare da Baraje kuma sun yi masa mubaya'a. Babu gudu babu ja da baya. Nan gaba ba da dadewa ba za'a yi babban taro a jihar Bauchi.
A jihar Gombe jigo a tafiya tare da Kawu Baraje Malam Garba Sale ya ce kowa ya yi na'am a wannan tafiyar a jihar Gombe. Ya ce mutane suna barin tsohuwar suna shigowa sabuwar. Ya ce nan ba da dadewa ba wadanda suke tare da Bamanga Tukur zasu bar shi su dawo sabuwar domin wasu sun soma fahimtar cewa gyara ake yi.Wata 'yar siyasa mai suna Halimar Iya Babba ta ce barakar da ta sa jam'iyyar ta dare dinkata sai ikon Allah sabili da manyan azzalumai suna so masu gaskiya ma suna so. Ta sa ma gwamnonin da suka dare albarka. Ta ce barakar ita ce alheri ga Najeriya domin an dade ana zaluntar irinsu talakawa.
Sai dai kuma jami'in PDP mai kula da harkokin jama'a a arewa maso gabas ya ce ba'a hana mutum ra'ayinsa amma ya ce duk wani ra'ayi da zaka yi ka yi na gaskiya. Ya ce menene za'a yiwa mutum har ya bar gidansu ya shiga tsinewa gidan. Ya yarda akwai baraka a jam'iyyar amma kuma ya ce suna iyakacin kokari su dinke wannan barakar.
Ga karin bayani.