Daraktan kula da raba Man Fetur na NNPC Mr. Nkem Obi, a zantawa da yayi da gidan Talebijin na Najeriya, NTA. yace Najeriya, na da wadatatcen Man da zai kai wata daya nan gaba da kamfanin ke dashi kuma ana daukar matakan wadatar da shi ga dukkan sassan Najeriya.
Shugaban kamfanin NNPC, Maikanti Kachala Baru, ya zaga yakunan Abuja, ya gano inda ake karkatar da Man ta hanyar sayarwa ‘yan bakar kasuwa.
Mutane kan hau kan layin neman Man fetur, su kwana har asuba kafin nasarar samun Man.
Wani gidan Man Total, dake daura da gidan Man NNPC, a Abuja da wakilin muryar Amurka Nasiru Adamu El-hikaya, ya ziyarta, ya samu mutane a dogon layi suna dakon a fara sayar da Man.
Shima a zantawarsa da NTA, sakataren kungiyar dillalan Man fetur IPMAN, Zanna Mustapha, yace kafa kananan matatun mai a Najeriya, na daga matakan kaucewa irin wannan kalubalen da yake faruwa domin dogaro da shigowa da Man daga ketare.
Mustapha, ya kara da cewa rashin wadatar Man, na kara kawo matsala da kuma dawainiyar dakon Man daga Legas zuwa jihohi masu nisa da hakan kansa kara farashin litar Man. A cewar sakataren dillalan kan sami fiye da farashin da aka kayyade domin haka yasa suke kara kudi daomin samun riba, ana rade radin cewa maiyuwa gwamnatin ta dawo da bada tallafi don Man ya wadata ko kuma yuwar kara farashin Man wannan shine harsashen da masana keyi da ake jiran samun haske daga gwamnati.
Your browser doesn’t support HTML5