Kungiyoyi arba’in na ‘yan awaren kasar Syria sunce ba zasu halarci taron sulhun da kasar Rasha zata shirya wata mai zuwa a birnin Sochi ba, suna mai cewa abin tsoro ne, ganin yadda Rasha ke kokarin kaucewa shirin Majalisar Dinkin Duniya na samar da zaman lafiya.
‘Yan awaren dai sunce Rasha na son suyi watsi da bukatarsu ta neman shugaban kasar Syria Bashar al-Assad ya sauka daga mulki.
Suka ce kamata yayi mai shiga tsakani ya zama adali kuma mai gaskiya. A matsayin Rasha na babbar kawar Syria, bata da su.
Rasha ta shirya zaman tattaunawar ranar 29 ga watan Janairu a birnin Sochi dake gabar tekun Bahar Aswad.
Gwamnati Syria ta ce zata halarci taron. Ita ma kasar Turkiyya wadda ke goyon bayan ‘yan awaren tace zata je taron, amma tace bai kamata ba a gayyaci kungiyoyin Kurduwa.
Yunkurin sasantawar da MDD ta sha yi a Geneva, hade da wasu tattaunawar daban nakasashen Rasha da Turkiyya da Iran ba suyi wani tasiri ba wajen kawo karshen yakin basasar shekaru shida na kasar Syria.
Facebook Forum