Kasar Masar ta kashe ‘yan ta’adda 15 da suka kai mummuman hari akan wani shingen sojoji dake zirin Sinai a shekarar 2013.
Kisan da aka yin a jiya Talata, an gudanar da su ne a gidajen Yari biyu dake a arewacin birnin Alkahira, wanda kuma shine kisan mutane mafi yawa da aka yi a Masar tun bayan rataye wasu ‘yan jihadi shida da aka samu da laifin ta’addanci a shekarar 2015.
Baki ‘daya mutanen 15 an kashesu ne ta hanyar rataya.
Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya umarci sojoji da su tashi tsaye domin murkushe ‘yan kungiyar ISIS, biyo bayan mummunan harin da yayi sanadiyar asaran rayukkan mutane sama da 300 da aka kai akan wani masallacin yankin Sinai a watan da ya gabata.
Facebook Forum