Navalny dai yayi kira ga magoya bayansa da kauracewa zaben da za ayi na ranar 18 ga watan Maris bayan da jami’an hukumar zaben kasar suka hanashi tsayawa takara.
Hukumar zaben kasar da ake kira da turanci Central Election Commision ko CEC a takaice, sun jefa kuri’ar kin amincewa da Navalny ya tsaya takara saboda kashin kajin da yake dashi game da aikata ayyukan assha na cin hanci da rashawa da ake tuhumarsa da shi.
Sai dai shi Navalny din da magoya bayansa sun ce wannan tuhumar ba komai ba ce illa tsagoran siyasa. Biyo bayan wannan matakin da hukumar zabe ta yanke kan Navalny, yasa shi fitar da wani faifa bidiyo inda yake kira da a kauracewa jefa kuria don a cewarsa, zaben na watan Maris ba zabe bane illa bankaura.
Mai magana da yawun shugaban kasar Rasha Dmitry Peskov ya fada yau cewa za a duba wannan kira na Navalny cikin tsanaki a gani idan hakan bai karya doka ba.
Sai dai tun farko Shugaba Puttin ya bayyana cewa zai sake tsayawa takara. Sannan abinda ake hashashe ga dukkan alamu zai yi nasara, wanda wannan shine zagayensa na hudu a matsayin shugaban kasar ta Rasha.
Facebook Forum