Al’ummar kasar Laberiya suka kada kuri’ar zaben shugaban kasa zagaye na biyu a zaben sabon shugaban kasar dake yammacin Afirka.
Fitatcen tsohon ‘dan wasan kwallon kafa George Weah da mataimakin shugaban kasa Joseph Boakai, sune ke fafatawa a zaben domin maye gurbin shugabar kasa Ellen Jonhson Sirleaf, wadda ke shirin sauka daga mulki bayan kammala wa’adi na biyu, wa’adin da kundin tsarin mulkin Laberiya ya bata dama.
Boakai da Weah sune suka sami kuri’u mafi yawa a zaben da aka yi ranar 10 ga watan Oktoba, inda Weah ya sami kashe 38.4 cikin 100 na kuri’un da aka jefa, shi kuma Boakai yazo na biyu da kashi 28.8 cikin 100 na kuri’un. Kasancewar baki ‘dayansu babu wanda ya sami kuri’u masu rinjaye, hakan yasa aka gudanar da zaben raba gardama, amma kalubalantar zaben da aka yi a kotu shine ya kawo tsaiko ga zaben da aka shirya yi tun farko ranar 7 ga watan Nuwamba.
Abokiyar takarar Weah itace Jewel Howard-Taylor, wata ‘yar majalisar dattijai ta Liberia kuma tsohuwar matar tsohon shugaban ‘yan tawaye kuma shugaban kasa Charles Taylor, mutumin da ya rura wutar yakin basasa a shekarar alif 989, wanda yanzu haka ke gidan Yari a Birtaniya, bayan da aka yanke masa hukuncin ‘daurin shekaru 50 kan rawar da ya taka a kisan kare dangi a Saliyo.
Facebook Forum