An kashe matashin ne da sauran mutane hudun a gaban jama’a ta hanyar bindigesu a shekaranjiya Lahadi a garin Idale mai tazarar kilomita 60 daga kudancin Baidoa, bayanda wani alkalin kungiyar al-Shabab ya yanke musu hukunci kisa bisa amsa laifinsu da aka ce sun yi.
Al-Shabab dai ta kashe jumular mutane 22 a wannan shekara, tara a cikin an kasha su ne bisa zargin leken asiri kana saura kuma a kan laifukar da suka hada da fiyade da luwadi da kuma sama da fadi da dukiya.
Kugiyar mai alaka da al-Qaida tayi shekaru da dama tana yunkurin kifar da gwamnatin Somalia domin ta samu damar girka tsarin Shari’ar Islama akan kasar.
Facebook Forum