Akwai Damar Kawo Sauyi A Tarihin Zirin Koriya -Pompeo

Mike Pompeo, sabon sakataren harkokin wajen Amurka

Yayinda da shugaban Amurka Donald Trump da na Koriya ta Arewa Kin Jong Un ke shirin ganawa, sabon sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ce gwamnatinsu zata sa ido ta tabbatar da an cimma nasara ta dindindin

Sabon sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo yace akwai wata gagarumar damar kawo sauyi a tarihin a zirin Korea, yayin da shugaba Donald Trump ke shirin ganawa da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un.


Pompeo yace gwamnatin Trump ba zata maimaita kura kuran da aka tabka a baya ba, ya kara da cewa ana zuba ido sosai. Yace sun muhimmantu wurin cimma nasara ta dindindin ta wargaza shirin makaman kare dangi na Korea ta Arewa, zamu yi haka bada bata lokaci ba.


Trum ya kai ziyararsa ta farko zuwa ma’aikatar harkokin wajen Amurka a jiya Laraba domin gudanar da bukin rantsar da sabon sakataren.