Ganawa da shugaban Koriyaa ta Arewa a yankin nan da aka hana harkokin soji,akan iyakan koriyoyin biyu zai kasance "da mamaki" inji shugaban Amurka Donald Trump, yana fadawa manema labarai a jiya Litinin, sa’o’I bayan sakon tweeter da ya aike a kan taron kolin da yake shirin yi da Kim Jong Un a ginin da ake kira "Peace House ko Freedom House" dake kan iyakar Koriya ta Arewa da ta Kudu.
Yace muna nazari a kan gudanar da taron a kasashe da dama ciki har da Singapore kana muna tattaunawa a kan yiwuwar yin taron akan iyakokin kasashen biyu inda aka hana harkokin soja, kamar yadda shugaba Trump ya fada a lokacin da ya gana da manema labarai tare da shugaban Najeirya Muhammadu Buhari a fadar White House.
Shugaban na Amurka yaki ya bayyana wasu wuraren da za a iya gudanar taron baicin Singapore da akan iyakokin koriyar biyu,Trump yace "labari mai dadi" cikin wannan lamari shine kowa yana so a taron a kasarsa.
Facebook Forum