Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Ya Bayyana Kwarin-guiwa Kan Alkawuran Kim Jon Un Na Koriya Ta Arewa.


Shugaba Trump da takwarar aikinsa ta Jamus.
Shugaba Trump da takwarar aikinsa ta Jamus.

Trump yace baya jin alkawuran irin wadanda koriya tayi a baya bane, baya jin wannan wasane, kuma Amurka ba zata kyale wannan karon a yi wasa da hankalinta ba.

Shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyana kwarin guiwa dangane da alkawaruan da shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jon Un yayi, a lokacinda ya gana da takwaran aikinsa na Koriya Ta Kudu a jiya Jumma'a.

"A'a, bana jin wasa yake yi, bana jin yana wasa ne," shugaba Trump ya fada a fadar White House, a kusa da shugabar kasar Jamus Angela Merkel. Zantuttukan basu taba yin nisa haka ba, Mr. Trump.

Shugaba Kim Jon Un, a jiya Jumma'a, ya zama shugaban Koriya Ta Arewa na farko da ya taba zuwa Koriya Ta Kudu, lokacinda ya tsallaka kan iyakar kasar, ya gaisa da takwaran aikinsa na Koriya Ta Kudu Moon Jae-in.

Shugabannin biyu sun amince suyi aiki wajen gani an kauda dukkan makaman Nukiliya daga zirin na koriya, kuma suka sha alwashin gudanar da shawarwari da zai kawo karshen yakin da kasashen biyu suka gwabza, wadda har yanzu ba'a kwance damara ba a hukumance.

A baya, Koriya Ta Arewa tayi irin wadannan alkawura dangane da shirin Nukiliyarta, amma kuma ta saba. Da aka tambayeshi ko yanzu alkawarin da Koriya Ta Arewa tayi da gaske ne, shugaba Trump, yace ba zamu "kyale a yi wasa da hankalin mu ba."

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG