Sabon sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, yace Amurka bata yanke shawara kan ko shugaba Trump zai janye Washington daga yarjejeniyar da manyan kasashen duniya suka kulla da Iran kan shirin Nukiliyar kasar, ya kara da cewa har yanzu ana ci gaba da gudanar da shawarwari.
A taron manema labarai na farko da yayi karkashin sabon mukaminsa, Pompeo yace, "muddin ba'a yiwa yarjejeniyar kwaskwarima ba, da zai shawo kan rauni dake tattare da ita, da wuya shugaba Trump ya ci gaba da mutunta yarjejeniyar gaba da watan Mayu mai zuwa." Mike Pompeo yayi magana ne a birnin Brussels a taron ministocin harkokin wajen kasashen da suke cikin kungiyar NATO, kwana daya bayan da aka rantsar da shi na fara aiki kan wannan mukami.
Pompeo, yace ya tattauna da takwarorinsa dangane da yarjejeniyar a kungiyar tsaron ta NATO. Babban jami'in difilomasiyyar ta Amurka yace wannan batu na iya kasancewa jigo a ajendarsa lokacinda ya kai ziyara yankin gabas ta tsakiya bayan kammala taron na NATO a Brussels.
Ahalinda ake ciki kuma, wata kusa a kungiyar tsaro ta NATOn tace minisotcin harkokin wajen wadannan kasashe ba zasu ci gaba da mu'amala da Rasha kamar yadda aka saba ba, har sai Moscow, ta janye dakarunta da goyon bayan da take baiwa 'yan tawaye a yankin Donbas, kuma ta sake maida yankin Crimea ga kasar Ukraine."
Wannan bukatu na ba safam ba, da kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Hearthert Nauert ta gabatar ta shafin Tweeter, yana zuwa ne a dai dai lokacinda sabon sakataren harkokin wajen na Amurka Mike Popmpe yake isa birnin Brussels- sako mai karfi da aka aikewa takwarorinsa a kungiyar ta NATO, a ranar da ya fara aiki kan wannan mukami.
Facebook Forum