Shugaban koriya ta kudu Moon Jae-in ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta sa ido a lokacin da koriya ta arewa ke rufe cibiyar gwajin makaman nukiliyarta dake Punggye-ri.
Wani mai magana da yawun Moon ya fada yau Talata cewa shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana ta wayar tarho da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Shugaban koriya ta arewa Kim Jong Un ya yi alkawarin rufe cibiyar a karshen watan nan na Mayu.
Wannan cigaba da aka samu na zaman wani bangaren matakan diflomasiyya da suka hada da wani babban taro da aka yi tsakanin Moon da Kim da kuma shirin ganawar da ake yi tsakanin Kim da Donald Trump.
Facebook Forum