Akwai Alamun Hannun Hama Amadou a Yunkurin Juyin Mulki

Hama Amadou

An gano wata takarda dauke da jerin sunayen wasu hafsoshin Soja

Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta bayyana cewa akwai alamun hannun tsohon kakakin majalisar dokokin kasa Hama Amadu, a yunkurin juyin mulkin da tace ta murkushe a watan jiya.

Ministan taron kasar Nijar Karidjo Mahamadou, ya bayana cewa bincike yana nuni da cewa akwai hannun masu damara 12, da farar hula daya, ya furta haka ne a wani ganawa da yayi da manema labarai inda yake bayani dangane da inda aka kwana a game da binciken yunkurin juyin mulki da Gwanatin Nijar, tace ta murkushe a watan jiya.

Ya kara da cewa an gano wata takarda dauke da jerin sunayen wasu hafsoshin Soja kimanin 10, a gidan daya daga cikin wadanda aka kama kuma a cewarsa akwai alamomi dake nuni cewa suna da hannu a wannan shiri.

Da yake amsa tambayar ko akwai hannun tsohon kakakin majalisar dokokin kasa Hama Amadu, a yunkurin juyin mulkin cewa yayi haka ne wasu daga cikin wadanda aka kama sun anbaci sunan sa kuma anje Filinge inda yake tsare an saurare shi, ya zuwa yanzu bani da cikakken bayani dangane da abubuwan da suka biyu baya sai da kuma idan bukatar a sake sauraronshi ta taso za’a koma can inda yake domin ya amsa tambayoyi.

Nan bada jimawaba za’a gurfanar da wadannan mutane gaban kotun Soja.

Sai dai kungiyoyin fararen hula sun fara kiran Gwamnatin ta Issoufu Mahamadou, tayi adalci ga wadanda bincike ya gano cewa babu hannun su a wannan yunkuri.