Mai martaban yayi wannan kiran ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a garin Potiskum kan makomar al’ummar masarautar nasa.
Mai martaban yace yanzu haka an soma samun zaman lafiya a wannan yanki, sai dai jamaa da dama sun tagayyara, wasu sun rasa muhallin su da dukiyar su baki daya don haka akwai bukatar wannan kwamitin ya waiwayi al’ummar nasu domin ceto su daga cikin wannan kangin.
Ga dai abinda mai martaban ke cewa.
‘’Ba shakka anyi hasaran rayuka, anyi hasarar dukiyoyi anyi hasarar muhallai, a gwamnatance akwai makarantu da wurare da aka kona a garin Potiskum ko a yanzu ma akace ana son mutanen nan da aka koro su a wurare daban-daban, su nan cike a garin nan.Wani yazo sai kaji tausayi wani lokaci dole ne muma mu sa hannu muga cewa mun tallaffa, haka ita ma gwamnati tasa hannu taga cewa ta tallafa’’.
Mai martaban ya mika godiyar sa ga dedekun jamaar da suke tallafawa wadannan jamaar a halin yanzu.
Ga Haruna Dauda Biu da Karin bayani