Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obama Ya Bayyanawa Amurkawa Halin da Kasa Take Ciki.


Obama African Leaders Initiative
Obama African Leaders Initiative

Abinda shugaban Barrack Obama yayi a cikin jawabin nasa shine bayani a takaice na abubuwan da yace zaiyi, ya kuma nuna wa Amurkawa cewa yayi wadannan abubuwan.

Amma kuma ya nuna musu cewa har yanzu akwai wasu abubuwa da yawa da suka rage za ayi.Musali abubuwan tattalin kasa na kasar, sai kuma abubuwan da suka shafi Karin ilmi, sana’oi da sauran su, da taimakawa ‘yan kasuwa da Amurkawa masu karamin karfi. Yadda za a taimaka musu, su samu suma su taso, da ‘yan makaranta yadda za’a rage kudin makaranta, da kuma yadda Amurka zata yi huldan jakancin diplomasiyya da sauran kasashen waje.

Aminu El-Yakubu ne Mazauni Amurka mai sharhi akan al’amurran yau da kullun, ke wannan bayanin sailin da suke zantawa da Grace Alheri Abdu game da jawabin da shugaba Obama yayiwa Amurkawa.

Da kuma Graceta tambaye shi ko yana jin cewa akwai bayanin da Amurkawa suke tsammani suji shugaban yayi amma kuma kila baiyi ba.

Anan sai Aminu yace Amurka babban kasa ce, wannan zai dogara daga wani sashen Amurka mutum yake ko kuma wsane matsala suke fuskanta domin kowa da raayin sa ko raayin ta.

Yace da yake lokacin siyasa ne akwai batutuwa da yawa.

Ga Grace Alheri Abdu da ci gaban hirar

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG