Karamar jakadiyar Nijar a Najeriya, Hajiya Rabi Dodo, ta bayyana gamsuwarta da yadda ake kyautatawa 'yan jamhuriyar Nijar dake zaune a cikin Jihar Bauchi.
A lokacin wata ziyarar da ta kai gidan gwamnati dake Bauchi, jakadiyar ta Nijar ta ce shugaba Mahamdou Issoufou ya tura ta musamman domin bayyana farin cikin yadda dangantaka ta 'yan'uwantaka take gudana a tsakanin Nijar da Najeriya da ma jihar Bauchi musamman.
Ta roki 'yan Nijar dake jihar da su yi tattaki zuwa garuruwan da aka ware musamman a lokacin zaben Nijar din domin su kada kuri'unsu, tana mai cewa akwai wasu garuruwa da dama a Najeriya da aka tanadi gudanar da zaben.
Gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar na Jihar Bauchi, ya bayyana farin cikin irin zaman 'yan'uwantaka da mutunta juna a tsakanin 'yan Nijar da Najeriya, yana mai fadin cewa akwai dangantaka mai karfi a tsakanin sassan biyu.
Yayi addu'ar Allah Ya sa a gudanar da wannan zabe na Nijar lami lafiya kuma cikin sa'a.