Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP Da Wasu Masanan Shari'a Sun Kushe Dage Zabe A Jigawa


Gwamna Mohammad Badaru Abubakar na Jihar Jigawa, arewacin Najeriya
Gwamna Mohammad Badaru Abubakar na Jihar Jigawa, arewacin Najeriya

Jam'iyyar PDP mai hamayya a Jihar Jigawa ta bayyana rashin jin dadinta da dage zaben kananan hukumomin da aka yi a jihar.

A lokacin da yake bayyana matsayinsu na yin watsi da hujjojin da hukumar zaben ta gabatar cewa ba ta da kudin da zata gudanar da wannan zabe kuma akwai rashin tsaro, mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP a Jigawa, Alhaji Aminu Jahun, yace "babu kudin ne hukumar zaben ta aika musu da jadawali har guda 15 na tsaida 'yan takara, kuma suka yi aiki da su tare da sa idanun hukumar?"

Alhaji Aminu Jahun yace idan har za a iya gudanar da zabe a Jihar Yobe, inda ake fama da mummunar matsalar tsaron da ta ninka ta jihar Jigawa, bai ga dalilin da zai sa a kawo irin wannan hujja domin dage zabe a jihar Jigawa ba.

Mukaddashin shugaban na PDP yace sun yi mamakin cewa a daidai lokacin da hukumar zaben zata tantance 'yan takarar da aka gabatar mata ne kawai kwatsam sai ta dage wannan zaben.

Yace zasu garzaya kotu domin neman hakkinsu game da wannan batun.

Barrister Audu Bulama Bukar yace lallai dokar zabe ta Jihar Jigawa ta ba hukumar ikon dage zabe idan tana da kwakkwaran zaton cewa za a samu tashin hankali, amma kuma tashe-tashen hankulan da suke faruwa a jihohin arewa maso gabas ai ba su shafi Jihar Jigawa ba.

Shi ma yace idan har za a iya gudanar da zabe a jihohin Borno da Yobe, bai ga dalilin da zai hana a gudanar da zaben a jihar Jigawa ba.

Martani Kan Jinkirta Zaben Kananan Hukumomi A Jihar Jigawa - 3'30"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG