Akalla mutum 20 ne suka mutu bayan da wani kwale-kwalen katako ya kama da wuta bayan ya yi bindiga a wani kogi a jihar Bayelsa da ke gabar tekun Najeriya a ranar Laraba, in ji kakakin 'yan sandan.
WASHINGTON, D. C. —
Kwale-kwalen dai na dauke da ‘yan kasuwa ne da ke kai kayayyaki zuwa yankunan bakin teku, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan Bayelsa Musa Muhammed ya bayyana a ranar Alhamis.
'Yan kasuwa kan yi tafiye-tafiye na mako-mako tsakanin matsugunan bakin teku da Yenagoa babban birnin jihar.
Akalla dai mutane 200 ne aka ruwaito sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Najeriyar a bara, inda hukumomi kan dora alhakin hakan akan cunkoso da rashin kula da matakan kare aukwar hadurra.
-Reuters