Wani mummunan hatsarin kwale-kwalen daya afku da yammacin jiya Lahadi a kogin Kwalgai dake karamar hukumar Auyo ta jihar Jigawa, yayi sanadiyar mutuwar mutum guda a yayin da aka yi nasarar ceto wasu 18, saidai har yanzu ana cigaba da neman wani mutumin daya bata.
Sanarwar da rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta fitar ga manema labarai, tace al’amarin ya faru ne da misalin karfe 10 da dare lokacin da ‘yan kasuwa kimanin su 20 daga kauyen Kwalgwai, suka hau kwale-kwale domin ketare kogin Kwalgwai.
Rahotanni sun bayyana cewa kwale-kwalen ya kife sakamakon igiyar ruwa mai karfi da kuma yawan lodi.
Sai dai daukar matakan gaggawa da gwanayen iyo da masunta da mutanen kirki da ayarin ‘yan sanda karkashin jagorancin baturen ‘yan sandan Auyo suka yi, ya sabbaba ceto fasinjoji 18 da ransu.
Sai dai anyi rashin sa’a, inda da fari aka ayyana cewa wasu fasinjoji mata guda 2 sun bata.
Amma, da sanyin safiyar yau Litinin 8 ga watan Yulin da muke ciki, aka tsinci daya daga cikin matan da suka batan, da aka bayyana sunanta da Habiba Ado, ‘yar shekara 18, daga kauyen Kwalgwai, nan take aka garzaya da ita zuwa asibitin garin Auyo, inda likitan dake aiki ya bayyana cewa ta mutu.
Rundunar ‘yan sandan ta bukaci mazauna yankin da matafiya su rika taka tsantsan tare da kaucewa yiwa kwale-kwale lodi fiye da kima, musamman a lokutan rashin kyawun yanayi, domin magance faruwar irin haka anan gaba.
Kakakin rundunar DSP Adam ya kara da cewa, muna yiwa iyalai da dangin wadanda suka rasu sakamakon wannan mummunan al’amari jaje da addu’o’in samun gafara.
Har yanzu hukumomin na cigaba da sa idanu akan lamarin, kasancewar an dukufa wajen neman ragowar fasinja guda da ta bata.
Dandalin Mu Tattauna