Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Hadarin Jirgin Ruwa A Mozambique Ya Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane Sama Da 90


AFPTV - Mutane 96 suka rasa rayukansu su a hadarin kwale-kwale a Mozambique (AFP/TVM)
AFPTV - Mutane 96 suka rasa rayukansu su a hadarin kwale-kwale a Mozambique (AFP/TVM)

Wani jirgin ruwan katako na tsalake kogi ya nutse a gabar tekun arewacin Mozambique inda ya kashe mutane 94, ciki har da yara, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito a yau Litinin.

WASHINGTON, D. C. - Silvério Nauaito, jami'in kula da tsibirin Mozambique, ya shaidawa gidan rediyon kasar Mozambique cewa, jirgin ruwan ya nutse ne da yammacin ranar Lahadi, kuma adadin wadanda suka mutu da a farko an dauka 91 ne, ya haura zuwa 94 bayan sake gano wasu gawarwaki uku a safiyar yau Litinin

AFPTV - Mutane 96 suka mutu Mozambique. (TVM/AFP)
AFPTV - Mutane 96 suka mutu Mozambique. (TVM/AFP)

Ya ce mutane 130 ne a cikin jirgin amma 94 sun rasa rayukansu kuma kusan mutane 11 suna jinya a asibiti."

"Akwai kusan wasu mutane uku da aka ceto, amma ba za mu iya bada tabbacin adadin nawa ne suka bace ba," in ji Nauaito ga gidan rediyon. Ya kara da cewa jami'ai na kan hanyarsu a ranar Litinin zuwa inda hatsarin ya afku domin samun cikakkun bayanai.

Jirgin ruwan da ke aiki tsakanin Lunga da ke lardin Nampula da tsibirin Mozambique ya cika makil, kuma da yawa daga cikin wadanda suka nutse yara ne, a cewar TV Diário Nampula, wata kafar yada labarai ta yanar gizo. Ya kuma kife a hanya.

Wasu daga cikin mutane sun yi balaguro ne don halartar wani bikin baje koli yayin da wasu ke kokarin tserewa daga Lunga zuwa tsibirin Mozambique saboda fargabar kamuwa da cutar kwalara, wadda ta shafi yankin a 'yan kwanakin nan, "in ji wata kafar labarai ta intanet.

Wasu rahotannin kuma sun ambato Jaime Neto, sakatariyar harkokin wajen kasar a lardin Nampula na cewa, rashin fahimtar da aka samu game da barkewar cutar amai da gudawa ya haifar da firgirtar wa tare da sanya mutane shiga cikin kwale-kwalen, wanda galibi a ake anfani da shiw wajen kamun kifi, don tserewa daga yankin.

Hukumomi a Mozambique da na makwabtan kasashen kudancin Afirka na kokarin shawo kan barkewar cutar kwalara da ta bazu cikin ‘yan watannin nan.

Yankuna da dama na Mozambique ana iya shigan su ne kawai ta jiragen ruwa, wadanda galibi suna da cunkoso. Kasar na da karancin hanyoyi kuma wasu wuraren ba a iya isarsu ma ta kasa ko ta sama.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG