AFCON 2025: An Saka Ranar Karawar Najeriya Da Libya

Super Eagles (Hoto: Facebook/Super Eagles)

Najeriya ita ce ta shida a iya taka kwallo a nahiyar Afirka yayin da Libya take matsayi na 33.

A hukumance, an fitar da ranakun da kungiyar ‘yan wasan Najeriya ta Super Eagles za ta kara da ta Libya a wasannin neman shiga gurbin gasar AFCON ta 2025.

Super Eagles za su karbi bakuncin wasan farko a ranar 11 ga Oktoba a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom.

Kwanaki hudu bayan wannan karawa kungiyoyin za su sake haduwa a Tripoli.

Super Eagles ce ke jagorantar Rukunin D da maki hudu bayan nasara ta 3-0 a gida akan Benin da kuma canjaras da suka yi da Rwanda a Kigali.

Libya tana rike da matsayi na karshe a cikin rukunin tare da maki guda daga adadin wasanni biyu da ta buga.

Najeriya ita ce ta shida a iya taka kwallo a nahiyar Afirka yayin da Libya take matsayi na 33.