Hamayya Ita Ce Kwalliyar Siyasa- inji Masana Demokradiyya

APC

Fiye da gwamnoni 20 ne jam’iyyar APC ta samu bisa ga sakamakon zaben bana. Haka zalalika jam’iyyar ta sami gagarumin rinjaye a zaben kujerun majalisar dokoki a yawancin jihohi, inda ma jam’iyyar ta sami dari bisa dari a majalisun dokokin jihohin Sokoto da Kano.

Masu nazarin harkokin demokradiyya na ganin cewa majalisun da jam’iyyar APC ta lashe zasu zama masu raunin gaske saboda rashin hamayya mai karfi, hamayyar da Masana kimiyar siyasa ke cewa itace kwalliya ko ruhin demokradiyya.

Farfesa Kamilu Sani fage, malami ne a sashen nazarin kimiyar siyasa a jami’ar Bayero dake Kano, ya fadi cewa duk inda aka sami jam’iyyar da ta kafa gwamnati kuma tana da ‘yan majalisa dari bisa dari, ‘yan majalisun zasu zama tamkar ‘yan amshin Shata ne.

Ya kara da cewa har yanzu ‘yan siyasa sun kasa bambance siyasa da kuma yi wa jama’a aiki. Abinda ya kamata shine sanya kasa ko jiha a gaba ba jam’iyya ba- a ta bakin Farfesa Kamilu.

Tun bayan da Najeriya ta dawo tafarkin demokradiyya, a shekarar aluf dari tara da cisi’in da tara ake zargin ‘yan majalisun dokoki da zama ‘yan amshin shatan gwamnoni.

Honarabul Alhassan Uba Idriss dake zaman tsohon wakili a majalisar dokokin jihar Kano, daga shekarar 2003 zuwa 2007, kuma tsohon wakili a majalisar tarayya daga shekarar 2007 zuwa 2011, ya fadi cewa ya kamata ‘yan majalisar su gane cewa kashi 70 na demokradiyya na karkashin su. Ya kuma ce ya kamata duk dan majalisar da zai shiga yanzu ya kawas da tsoro, da son abin duniya yayi karatun baya ganin abinda ya faru da jam’iyyar PDP.

Ga karin bayani daga Mahmud Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

Hamayya Ita Ce Kwalliyar Siyasa- inji Masana Demokradiyya