Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda ta Kaya a Jahohin Bauchi da Gombe


sakamakon zabe.
sakamakon zabe.

Wata sabuwar al’adar da yan takarar siyasa a Najeriya suka dauka itace kiran abokan takarar su domin taya su murnar lashe zabe kamar yadda tsohon Shugaban kasar Goodluck Jonathan yayiwa zababben shugaban janar Muhammadu Buhari.

Wata sabuwar al’adar da yan takarar siyasa a Najeriya suka dauka itace kiran abokan takarar su musamman idan sun fadi zabe domin taya su murna.

A jahohin Bauchi da Gobe, Auwal Jatau daga jam’iyar PDP da kuma Alhaji Inuwa Yahaya na jam’iyar APC , dukkan su sun amince da sakamakon zaben da hukumar zabe ta bayar tare da taya wadanda sukayi nasara murna.

Muhammad Auwal Jatau na jahar Bauchi kamar yadda rahoton wakilin sashin Hausa na murayar Amurka Abdulwahab Muhammad ya aiko mana, yace “Na nemi ganawa daku ne domin nuna shaidar godiya ta musamman ga ubangiji da ku gabadaya. Nasan al’amarin ubangiji ne shike badawa kuma shike hanawa, dan haka ina taya barista M.A Abubakar murnar lashe wannan zabe da yayi kuma Allah ya taya shi ruko.”

Shima Alhaji Inuwa Yahaya a jahar Gonbe ya taya Ibrahim Hassan Dan Kwambo murnar lashe wannan zabe karo na biyu. Yayi bayanin cewar ya aminta da harkar demokaradiyya shiyasa ya shiga zabe, kuma ya kara da cewar ya yadda da duk abin da Allah yayi a atsayin sa na musulmi duk da yake baikira shi ta way aba amma yana taya shi murna.

Zababben gwamnan Ibrahim Hassan Dan Kwambo a jawabinsa na godiya ya bukaci neman hadin kai domin a yiwa mutane aiki. Jiya ne dai jahar ta Gombe ta fitar da sanarwar takaita fita wadda ta kafa a jahaer kimanin wata guda da ya wuce.

ZABEN 2015: Yadda ta Kaya a Jahohin Bauchi da Gombe - 3'52"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG