Kwanaki kadan bayan aukuwar lamarin, wasu daga cikin ‘yan matan su 50 sun kubuta daga hannun ‘yan bindigar sun kuma bayyana cewa an tsare su ne a dajin Sambisa dake jihar Borno.
Biyo bayan bayyanuwar labarin, kungiyoyi masu zaman kansu su a gida Najeriya da ma kasashen waje suka fara matsa lamba ga mahukuntan Najeriya don a ceto ‘yan matan. Daya daga cikin kungiyar itace ta Bring Back our Girls, wadda ta kwashe kusan shekara daya tana zaman dirshan a dandalin Unity Fountain dake birnin tarayya Abuja.
Fatima Abbah Kaka, jigo ce a kungiyar ta fadi cewa suna nan kan bakansu, ba za su daina yin kira da a ceto daliban ba don basu fidda rai ba kuma babu abinda ya fi karfin Ubangiji.
Yau 14 ga watan Afrilu ne shekara daya cur da sace ‘yan matan, abinda ya sa kungiyar ta Bring Back our Girls yin wani gangami da ya kunshi iyaye da dalibai domin tunawa da wannan rana mai juyayi.
Mrs. Martha Enoch na daya daga cikin wadanda suka halarci wannan gangamin, ta fadi cewa ‘yayanta biyu, Sarah da Monica na cikin wadanda aka sace. Mrs. Martha kuma tace har yanzu ita da iyalinta suna cikin juyayin abinda ya faru.