Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sace Daliban Chibok Ya Tada Hankalin Duniya-Aminu Gamawa


Rebeccca Samuel (tsakiya), mahaifiyar Sarah, daya daga cikin daliban na Chibok da aka sace, tana zaune tare da wasu iyayen a lokacin wani taron da suka yi domin tattauna kokarin kwato 'yan matan na Chibok da aka sace.
Rebeccca Samuel (tsakiya), mahaifiyar Sarah, daya daga cikin daliban na Chibok da aka sace, tana zaune tare da wasu iyayen a lokacin wani taron da suka yi domin tattauna kokarin kwato 'yan matan na Chibok da aka sace.

Yau shekara daya ke nan cur da 'yan Boko Haram suka sace daliban makarantar 'yan mata a garin Chibok jihar Borno.

Aminu Gamawa yace an jima ba'a samu alamarin da ya jawo hankalin duniya kamar sace daliban Chibok ba.

Kasashen duniya da kafofin labaru da dama da kungiyoyi masu zaman kansu sun tashi haikan wajen ganin cewa sun yi magana amadadin yaran kuma sun yi kira ga ita gwamnati da ta ga cewa an kwato yaran a kuma hadasu da iyayensu.

Abun tausayi kuma abun takaici, kuma abun banhaushi shi ne yau watanni goma sha biyu ko makonni hamsin da biyu, ko kwanaki 365, wato shekara guda cur yaran nan basa hannun iyayensu. Suna hannun 'yan Boko Haram. Ba'a kwatosu ba ba'a kuma bada wani cikakken bayani ba kan yadda suke ba. Wannan ba karamin abun banhaushi ba ne.

Aminu Gamawa ya cigaba da cewa basu kadai 'yan Boko Haram suka sace ba. Kafinsu an sace 'yan mata an sace yara. Bayansu ma an sake sace yara da 'yan mata. Ana anfani da 'yan matan Chibok wajen nuna gazawar gwamnatin tarayyar Najeriya tare da rashin tsaro da ake fama dashi a arewa maso gabashin kasar.

Iyaye da dama suna zama cikin zullumi. Suna tsoron tura 'ya'yansu makaranta ganin cewa babu cikakken tsaro.

A lura, tunda abun ya faru iyayen yaran su ma basu zauna ba. Wasu ba zasu iya yin sana'o'insu ba. Wasu ma rashin lafiya daban daban ya kamasu. Kodayake abun ya faru shekara guda da ta gabata, har yanzu mutane basu manta ba kuma suna cikin haushi .

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:19 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG