‘Yan Najeriya na ci gaba da bayyana ra’ayoyi mabanbanta a yankin kudu maso gabashin kasar dangane da sake kama shugaban kungiyar IPOB Nnamdi Kanu da hukumomin kasar suka yi.
Hakan na faruwa ne yayin da hukumomin Najeriya ke kokarin maido da cikakken zaman lafiya a yankin.
A ranar Talata Ministan shari’a Malami Abubakar ya bayyana cewa an cafke Kanu wanda yanzu haka yana tsare a ofishin jami’an DSS yana jiran shari’a.
Ko da yake ministan bai fadi inda aka kama Kanu da kuma yadda aka kama shi, amma tuni har an gurfanar da shi a gaban kotu a ranar Talata.
"Idan ana masa shari'a ne bisa tanadin doka, toh zan ce babu matsala. Amma idan ana masa shari'a ne ta fuskar yanayin da kasar ke ciki yanzu, cewar wannan gwamnatin na farautar mutanen kudu maso gabas, to fa ina hangen hadari." In ji Wani mai sharhi, Dakta Celestine Nwosu.
Karin bayani akan: Nnamdi Kanu, Biafra, IPOB, Malami Abubakar, Ministan Shari’a Abubakar Malami, DSS, Nigeria, da Najeriya.
Kama Kanu na zuwa ne a daidai lokacin da ake yawan samun arangama tsakanin ‘ya’yan kungiyar IPOB da Kanu ke jagoranta da jami’an tsaro.
"Ko da yake fafutukar da yake yi don balle wa daga kasar, bai kamata ya dauki mayaka ba. Wannan tsarin bai yi ba kwatakwata. Ni dai ina mai ra'ayin cewa kamata ya yi ya fuskanci shari'a. A takaice dai na goyi bayan kama shi da aka yi, amma ban goyi bayan a yi masa wata illa ba," in ji Mista Emeka Onah wanda ke sharhi kan al’amuran yau da kullum.
Shi kuwa Mista Ugochukwu Ogbonnaya malamin jami’a cewa ya yi bai kamata a dawo da Nnamdi Kanu Najeriya a wannan lokacin da ake kokarin murkushe ayyukan 'yan kungiyar awaren ba.
"A ganina wannan ba daidai lokacin da ya kamata a kama shi ba ne, ganin irin damuwar da kasar ta ke ciki. Don guje wa zafafa yanayin fargaba a kasar, ba na tunanin ya dace hukumomi su sake kama shi a wannan lokacin, saboda akwai fushi a ko'ina. Bai kamata ba."
Tun ranar Lahadin da ta wuce ne aka dawo da Nnamdi Kanu Najeriya, kamar yadda Ministan Shari'ar kasar Abubakar Malami ya tabbatar. Kuma an riga an gurfanar da shi a gaban kuliya, wacce ta bai wa gwamnatin kasar damar ci gaba da tsare shi.
Yanzu ana tuhumar Nnamdi Kanu ne da cin amanar kasa da hada kungiyoyin ta da-zaune-tsaye, da mallakar makamai ba bisa ka'ida ba, da shigo da haramtattun kaya, da kuma yada labaran karya, kamar yadda Ministan Shari'a ya bayyana.
A shekarar 2017 aka ba da belin Nnamdi Kanu, inda daga baya ya tsallake ya fice daga kasar bayan wani samame da dakarun Najeriya suka kai gidansa a Umuahia da ke jihar Abia.
Hakan ya sa a shekarar 2019, kotun ta soke belin da ta ba shi.
Amma yayin zaman kotun da aka yi a ranar Talata, Nnamdi Kanu ya fadawa kotun cewa ya tsere ne domin yana fargabar za a salwantar da rayuwarsa kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito.
Nnamdi Kanu: An Cafke Shugaban Masu Fafutika Raba Najeriyar, Za a Tuhume Shi
Your browser doesn’t support HTML5