Shugaba Buhari ya umarci hafsoshin tsaro na kasar su dauki matakai na gaggawa na murkushe 'yan ta’adda masu satar mutane da wadanda suke hana zaman lafiya a sassan kasar domin tabbatar da ganin an kawo masalaha da cikkaken tsaro a kasar.
Wannan umarnin yana zuwa ne yayin da shugaba Buhari ya gana da hafsoshin tsaron a shirye-shiryen da ya ke na tafiya zuwa kasar Burtaniya domin duba lafiyarsa.
Karin bayani akan: London, Korona, Burtaniya, Boko Haram, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Jim kadan bayan kammala ganawar a ranar Talata shugaban ya hau jirgi ya tafi Burtaniya kamar yadda wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya aikawa manema labarai a ranar Litinin ta ce.
Sai dai sanarwar ta Adesina, ba ta ambaci ko shugaba Buhari zai bawa mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbanjo rikon kwarya ba kafin ya dawo.
A wurin taron Shugaba Muhammadu Buhari ya fadawa hafsoshin tsaron cewa lokacin ya yi da su ne za su fara kai hare-hare ba wai su tsaya suna kariya ba har sai an kawo mu su hari.
Ya ce ya kamata a dau matakai na karfafa zuciyar ‘yan Najeriya da imaninsu cewa hafsoshin tsaro da sauran jami’an tsaro na kasar suna iya kare su daga miyagun mutane da ke hana ruwa gudu a cikin Najeriya.
A lokacin da ya ke ganawa da manema labarai mai bawa Shugaban Najeriya Shawara a sha’anin tsaro, Manjo Janar Babaga Manguno, ya ce shugaba Buhari ya fito fili ya nunawa dukan jami’an tsaro da masu leken asiri cewar su dauki mataki na farko wanda zai tabbatar da sun zakulo shugabannin ‘yan ta’addan da wadanda suke daure musu gindi ko kuma mara musu baya domin hana su ci gaba da kawo tashe-tashen hankula a sassan Najeriya.
Mangonu ya kara da cewa shugaban ya ce ba za’a yadda da ci gaba da halin ko in kula a kan yadda ‘yan ta’adda suke matsawa al’umma ba tare da hafsoshin tsaro da sauran jami’an tsaro baki daya sun dauki matakai don a hana su walwala ba, a kuma kai musu hari ba jira sai sun kawo hari sannan ayi kariya ba.
Mangonu ya ce shugaban ya bada tabbacin cewa an dauki matakan da suka kamata domin a tabbatar da ganin an bai wa jami’a tsaron Najeriya dukan makaman da suka kamata domin samun nasarar wannan aiki.
Dangane da masu tashe-tashen hankula ko ingiza mutane a yi tarzoma ko a raba Najeriya, Shugaba Buhari ya umarci hafsoshin tsaro na kasar su dauki duk matakin da ya kamata bisa ga doka a zakulo ire-iren wadannan mutane a murkushe su kuma ayi musu hukunci gwargwadon yadda dokokin kasar suka tanada ba tare da an ci gaba da yin kace-nace na kawo tashin hankali a cikin Najeriya ba.
Saurari cikakken rahoton Musa Farouk Musa:
Your browser doesn’t support HTML5