Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Tafi London


Shugaba Buhari
Shugaba Buhari

An jima rabon da a ga shugaban na Najeriya ya je kasar ta Burtaniya domin duba lafiyarsa.

Buhari ya kama hanya ne da tsakar ranar Talata bayan da ya kammala taro da manyan jami'an tsaron kasar.

A lokacin taron, ya yi kira ga jami’an tsaron da su fatattaki ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da kuma masu daukar nauyinsu.

Shugaban na Najeriya mai shekara 78, zai je kasar ta Burtaniya ne don ganin likitansa, kamar yadda wata sanawar da fadarsa ta fitar da maraicen ranar Litinin ta ce.

Shugaban Najeriya, lokacin da ya kama hanyar zuwa London 03/30/21 (Hoto: Fadar shugaban Najeriya)
Shugaban Najeriya, lokacin da ya kama hanyar zuwa London 03/30/21 (Hoto: Fadar shugaban Najeriya)

“Yayin taron da ya yi da manyan hafososhin soji da sauran jami’an tsaro a yau, @MBuhari, ya ba su umurnin su fatattaki ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da masu daukar nauyinsu.” Bashir Ahmad da ke ba shugaban shawara kan kafafen sada zumunta ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Talata.

Karin bayani akan: London, Korona, Burtaniya, Boko Haram, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Baya ga matsalar mayakan Boko Haram a arewa maso gabashi, arewacin yammacin Najeriya na fama da matsalar ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

“Dole ne a kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane ba tare da bata lokaci ba,” Buhari mayna jami’an tsaron kasar.

Hotunan Taron Majalisar Tsaro Da Buhari Ya Jagoranta Kafin Tafiyarsa Zuwa London
Hotunan Taron Majalisar Tsaro Da Buhari Ya Jagoranta Kafin Tafiyarsa Zuwa London

A tsakiyar watan Afrilu ake sa ran shugaban na Najeriya zai dawo daga London, inda ya saba zuwa don ganin likita.

An jima rabon da shugaban na Najeriya ya je kasar ta Burtaniya domin ya duba lafiyarsa.

Har yanzu fadar ta Aso Rock ba ta fadi takamaiman abin da ke damun shugaban na Najeriya ba, wanda ya tafi neman maganin yayin da likitocin kasar ke shirin shiga yajin aiki a ranar 1 ga watan Afrilu.

XS
SM
MD
LG