Rahotanni daga Najeriya na cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai yi tafiya zuwa London a gobe Talata don duba lafiyarsa.
“Shugaba Buhari zai je London a ranar 30 ga watan Maris domin duba lafiyarsa kamar yadda ya saba,” wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya aikawa manema labarai a ranar Litinin ta ce.
Sanarwar ta kara da cewa, shugaba Buhari zai fara ganawa da manyan hafsoshin tsaron kasar," kafin daga bisani kuma sai ya kama hanya,” zuwa London.
“A mako na biyu cikin watan Afrilun shekarar 2021 zai dawo,” a cewar Adesina.
Karin bayani akan: Yemi Osinbajo, Dr. Abu Yazid, Korona, Burtaniya, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Sai dai sanarwar ta Adesina, ba ta ambaci ko shugaba Buhari zai ba mataimakinsa Prof. Yemi Osinbajo rikon kwarya ba kafin ya dawo.
Lokaci na karshe da Buhari ya je London don ganin likitansa shi ne a ranar 8 ga watan Mayun 2018, inda ya dawo bayan kwana hudu.
Gabanin hakan, ya yi wani balaguron a ranar 7 ga watan Mayun 2017 zuwa London don duba lafiyarsa, inda ya kwashe kwana 104 kafin ya dawo a ranar 19 ga watan Agusta.
A lokacin da ya dawo ya, shugaban ya fara aiki daga saboda a cewar jami’an fadarsa, “beraye sun yi barna a ofishinsa.”
Tafiyar ta Buhari na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar likitocin kasar ta bayyana shirinta na shiga yajin aiki a ranar Alhamis, idan har ba a biya mata bukatunta ba.
Bukatun da ta gabatar sun hada da rashin biyan mambonbinta cikakken albashinsu da alawus-alawus da suke bin gwamnati a matakin tarayya da na jihohi.
Batun zuwan shugaban na Najeriya ganin likita a kasar waje, ya jima yana janyo suka daga wasu jama’ar kasar da bangaren ‘yan adawa, wadanda suke kira da a inganta asibitin fadar shugaban kasar maimakon zuwa kasashen waje.
Ba a Najeriya kadai ba, shugabannin kasashe masu tasowa musamman a Afirka kan fita kasashen ketare ne a duk lokacin da suka bukaci ganin likita.