Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mun Tattauna Da Buhari Akan Matsalar Tsaro - Kayode


Gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ya gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buharu a fadar Aso Rock kan lamuran tsaro.

Fayemi wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnoni, ya tattauna da shugaban kan batun odar makamai inda ya ce nan gaba kadan shugaban zai tura kuduri gaban majalisa don sayo makamai.

Duk da wannan bai shafi rashin ganin makamai a kasa ba, kamar yanda mai ba da shawara kan tsaro Babagana Monguno ya fada, amma ya nuna akwai damuwa cewa miyagun iri kan mallaki makamai masu illar gaske da tunkarar su sa an shirya sosai.

Karin bayani akan: Babagana Monguno, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Fayemi ya nemi ture tunanin jama'a cewa shugaba Buhari bai san ainihin abun da ke faruwa a kasar ba, ya ce a zantawar sa da shugaban ya fahimci shugaban ya san duk abun da ke faruwa a Najeriya, har ma da wasu bayanai da ba a sani ba.

Fayemi ya kara da cewa, Shugaba Muhammadu Buhari yana da masaniyar abubuwan da ke wakana a kasar, fiye da tunanin mutane. Bisa ga cewarsa, shugaban ya amince da samawa dakarun tsaro kayan aiki don taimakawa sabbin manyan hafsoshi su cimma nasarar samar da tsaro mai inganci.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG